An Hori Yan Jarida Kan Rahotonnin Da Zasu iya Haifar DaTashin Hankali

Cibiyar Fasahar Sadarwa Da Ci Gaban Jama’a wato Centre For Information Technology and Debelopment (CITAD) ta jinjina wa hukumar gudanarwa na kafar sadarwar Premium Times a bisa daukan matakin gaggawa kan dan rahotoninsu da ya wallafa labarin karya marar tushe a jihar Filato. Jami’in CITAD a jihar Bauchi Mohammed Chiroma Hassan shine ya bayya hakan a jiya Talata sa’ilin da yake bayani wa ‘yan jarida dangane da illar yada rahotonin karya da kalaman batanci da wasu kafafen sadarwa ke yi, inda cibiyar ta bayyana cewar da bukatar ‘yan jarida su hada hanu domin dakile irin wannan lamarin da ke kawo wa kasar nan ci baya. Mohammed Chiroma Hassan ya ce; “Guje wa yada kalaman batanci da karerayi hadi da hotunan da suke hargiza jama’a abu ne wanda ya hau kan ‘yan jarida da al’umma domin kawar da su. “Yada labaran karya a cikin al’umma musamman wanda kafafen sadarwa suke yi na matukar jefa wa jama’an kasa firgici da tashin hankali, don haka da bukatar a hada hanu waje guda domin kawar da irin wannan dabi’ar,”

In ji CITAD. Jami’in Cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban, ya kuma bayyana cewar wajibi ne a tashi tsaye domin nusar da jama’a illolin da kafafen sadarwar zamani ke haifarwa a kasar nan, inda ya bayar da misali da tashin hankalin da aka samu a Jos kwanakin nan, “Abun da ya jawo hankalinmu kan hakan, shine yadda wasu ‘yan jaridu ke yada kalaman batanci da labarai marasa sahihanci da nagarta, ku dubi yadda rahoton karya ya jawo tashin hankali a jihar Filato,” In ji shi. Chiroma ya bayyana cewar akwai hanyoyin sadarwar zamani da ake iya bi domin tantance sahihancin hoto ko labarin da ka iya kawo rudani a tsakanin jama’a, “Dukkanin kafafen sadarwar nan, akwai yadda ake tura musu bayani kan labari kaza ko hoto kaza baida sahihanci, za su dauki matakin sharewa cikin kasa da awa 24, muna kokarin koyar da jama’a hanyoyin da za su bi wajen yin hakan,” in ji Muhammad Hassan.

Ya kara da cewa; “Labarin kwanan nan da jaridar Premium Times ta wallafa; shi wannan labarin da dan rahotonsu ya basu labarin karya ne ya shirya, bai yi hira da kowa ba ya harhada labarinsa wai kisan da aka samu a jihar Filato na zuwa ne a sakamakon kashe-kashen shano da aka yi; alhali wannan da ya yi amfani da sunansa wai Mr. Chiroma na kungiyar Miyetti Allah, ya ce wai kisan an yi ne a matsayin ramuwar gayya, alhali karya ne muraran. “Ita gidan jaridar ta Premium Times ta binciko labarin inda ta fahimci dan rahotonta ya sharara karya, don haka ta dauki matakin baiwa jama’a hakuri da kuma hukunta wakilinnata. A dunkule muna jinjinawa matakin da gidan jaridar ta dauka, muna kuma kira ga sauran gidajen jaridu su dauki irin wannan matakin idan hakan ta faru domin kawo karshen shigar wa jama’a da rahotonin karya da kuma kage wanda ka iya haifar da tashin-tashina a cikin al’umma,” In ji CITAID.

Cibiyar ta kuma shaida cewar kafafen sadarwar zamani suna da karfin da suke isar da sako wa jama’a cikin kankanin lokaci; inda cibiyar ta bayyana cewar wannan damarce take baiwa kafafen sadarwar zamani damar yada shirme da karerayi domin cimma muradin wasu marasa kishin kasa. Ya ce, ya kamata jama’a suke yarda da sahihancin labara kadai in suka gani a jarida mai nagarta ba wai kafafen da ka iya kawo tashin hankali kai tsaye ba. Muhammad Ciroma ya bayyana cewar sun fito da hanyoyin da suke bi wajen rage kaifin makamancin wannan lamarin, inda ke bayani da cewa, “Abubuwan da muke yi wajen dakile irin wadannan labaran karyan suna da yawa, mukan bibiyi irin kamalan bantanci da ake yi a yanar gizo-zizo da kuma gidajen jaridu, domin muna da jami’an da suke sanya ido kan irin wannan.

A kowace karshen wata muka zauna mu tattaro labaran mu fadakar da ‘yan jaridan da kuma gwamnati, hade da al’umma, su al’umma muna nusar da su yadda za su yi wajen yakar irin wannan labaran batancin,” In ji Ciroma. Cibiyar ta kuma yi amfani da taron manema labaru wajen yin kira ga ‘yan jarida da a kowani lokaci suke bin ka’idojin da dokokin aikinsu, hadi da cire son zuciya wajen bayar da rahoton abun da suke son yadawa, sun nemi gwamnatin kuma ta tashi tsaye wajen kawo karshen kalaman bantanci hadi da rahotonin da za su haifar da kiyayya a tsakanin al’umma.

CITAD bata kuma tsaya haka nan ba; ta nemi jama’a da suke kaurace wa dukkanin wani rahoton da basu gamsu da sahihancinsa ba, kana suke amfani da hakan wajen kauda kansu kan kowace irin labarin da suke gani da ka iya kawo tashin hankali a tsakanin al’umma domin ci gaban kasar Nijeriya da jama’an kasa.