CITAD ta ƙaddamar da manhajar da za a dinga amfani da ita wajen kai rahoton cin zarafin mata

 

A Æ™oÆ™arin ta na yaÆ™i da mummunar É—abi’ar nan ta cin zarafin mata da kananan yara, cibiyar bunÆ™asa fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD), ta Æ™addamar da wata manhaja da za a dinga amfani da ita wajen saka ido tare da kai rahoton cin zarafin mata a kowanne lokaci.

Cibiyar ta CITAD ta ƙaddamar da wannan manjahar ne a yau Alhamis a ofishinta da ke Kano, da nufin samun cikakken bayani tare da adadin waɗanda ake ciwa zarafin a cikin makarantun da ke jihar Kano.

Haka kuma cikakken bayanin da manjahar za ta tattara zai baiwa mahukunta da Æ´an jarida da kungiyoyin fararen hula da kuma Æ™ungiyoyin mata wajen Æ™ara fahimtar yadda ake samun Æ™aruwar wannan mummunar É—abi’ar tare kuma da Æ™ara taimakawa wajen wayar da kan al’umma da Æ™ara samar da dokokin da za su baiwa mata kariya.

Jami’i a É“angaren fasaha na Cibiyar ta CITAD, Suhail Sani Abdullahi ya bayyana cewa samar da wannan sabuwar manhajar zai taimaka wajen karÉ“ar rahoto daga wakilan sa kai da aka naÉ—a a makarantu tare da adana bayanai yadda ya kamata.

Suhail Sani ya Æ™ara da cewa cibiyar ta CITAD ta himmatu wajen aiki tare domin ganin mata da Æ™ananan yara sun samu aminci daga wannan mummunar É—abi’a.

Haka kuma Suhail ɗin ya ƙara da cewa manjahar ba za ta taɓa ambata sunan wanda ya kai rahoton ko aka ci zarafinsa ba, kuma manjahar za a sameta a manhajar Google Play a cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

A nasa bangaren babban daraktan cibiyar ta CITAD, Injiniya Yunusa Ya’u bayyana damuwarsa ya yi akan yadda ake Æ™ara samun Æ™aruwar wannan mummunar É—abi’ar a tsakankanin mata da Æ™ananan yara a jihar Kano.

Injiniya Yunusa Ya’u ya ce akwai buÆ™atar a haÉ—u guri guda domin yaÆ™i da wannan mummunar É—abi’ar.

“Cin zarafin mata babbar matsala ce a cikin al’umma, kuma ana yin wannan dabi’a ne ta fuskoki daban – daban kama daga kan fyade a makarantu da auren wuri da cin zarafin mata domin a ba su maki ko aikin yi da sauran dangogin wannan miyagun É—abi’u”

Ya Æ™ara da cewa “Ana samun irin wannan cin zarafin a zahiri da kuma shafukan sadarwa na zamani wanda cin zarafin kan cutar tare da jefa rayuwar mata cikin mummunan hali”
Injiniya Yunusa Ya’u ya ce bayanan da wannan manhaja za ta tattara za a yi amfani da shi wajen Æ™ara wayar da kan al’umma da kuma shigo da masu ruwa da tsaki wajen yaÆ™i da cin zarafin matan.

Haka kuma za a yi amfani da bayanan wajen koyar da mata dabarun kare kai tare da kaucewa fadawa komar masu aikata wannan mummunar É—abi’ar da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da aikata wannan dabi’a a gaban hukuma domin ya fuskanci shari’a.

A nata É“angaren Zainab Aminu wacce ita ce jami’ar da ta ke kula da shirin na yaÆ™i da cin zarafin mata da cibiyar ta CITAD ke gabatarwa wanda ya ke samun tallafi daga gidauniyar Ford, godewa É—aliban da su ka halarci taron Æ™addamar da manhajar ta yi tare da bayyana cewa hakan zai ba su damar fahimtar illar da ke tattare da cin zarafin mata da kuma kai rahoto cikin sauÆ™i.

Zainab Aminu ta ce hakki ne da ya rataya a wuyan kowa wajen kai rahoto tare da yaÆ™i da wannan mummunar É—abi’ar da ta zame wa al’umma annoba.

Ana samun ƙaruwar cin zarafin mata da ƙananan yara a jihar Kano, domin ko a cikin watan Janairun shekarar nan sai da hukumar Hisba ta jihar ta bayyana cewa ana samun ƙaruwar cin zarafin matan daga mazaje.

Taron dai ya samu halarcin dalibai daga jami’o’i da sauran manyan makarantu da ke faÉ—in jihar Kano.