CITAD ta samu tallafi daga gidauniyar MacArthur game da allurar riga-kafin Korona

A ƙoƙarinta na ganin al’umma sun karɓi riga-kafin allurar riga-kafin cutar Korana a yankin arewacin Najeriya, gidauniyar MacArthur da ke ƙasar Amurka ta baiwa cibiya bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, tallafin kuɗi domin cigaba da wayar da kan al’umma wajen karɓar riga-kafin cutar a yankin Arewacin Najeriya.

Gidauniyar ta MacArthur ta sanar da bayar da tallafin kuɗi kimanin Dalar Amurka miliyan 80 a matsayin taimokonta akan yaƙi da annobar korona da ta addabi duniya.

Shugaban gidauniyar ta MacArthur John Palfrey ya bayyana cewa la’akari da halin da aka fito da kuma yadda annobar ta Korona ta yi tasiri ga abubuwan da su ke alaƙa da rayuwar al’umma kuma suna buƙatar farfaɗowa ya sanya ta bayar da tallafin domin tsarin gidauniyar ta su ne haka.

John Palfrey ya ce gidauniyar ta himmatu wajen ganin bayan wannan annoba ta hanyar bayar da tallafi domin farfaɗo da inda cutar ta yiwa illah, da kuma cigaba da wayar da kan al’umma wajen ganin sun karɓi riga-kafin cutar ta Korona.

Cibiyar CITAD dai na ɗaya daga ƙungiyoyin da su ka samu tallafin akan yaƙi da cutar ta Korona tare da wayar da kan al’umma akan irin alfanun da ke tattare da riga-kafin cutar.

Idan za a iya tunawa dai tuni kwamitin fadar shugaban ƙasa kan yaki da annobar Korona a ƙasar nan ya ware jihohi shida da babban birnin tarayya Abuja a matsayin yankuna mafiya hadari da ake fargabar barkewar cutar zagaye na uku.

Jihohin sun hada da Lagos da Oyo da Rivers da Kaduna da Kano da Plateau da kuma Abuja fadar gwamnatin kasar nan.