Fiye da kashi 50 na É—alibai mata da ke manyan makarantu a Kano na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata

Cibiyar Wayar da kan Al`umma akan Shugabanci na gari da Tabbatar da Adalci (CAJA), ta bayyana cewa fiye da rabin dalibai mata da su ke karatu a makarantun gaba da sakandire a jihar Kano suna fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata daga malaman da su ke koya musu da kuma ma’aikatan makarantun.

Babban daraktan cibiyar Kabiru Saidu Dakata ne ya bayyana haka, a lokacin da ake gudanar da taron ƙarawa juna sani da Gidauniyar Rosa Luxemburg mai kula da Yammacin Afrika ta ɗauki nauyin gudanarwa tare da haɗin gwiwar Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani da ci gaban al`umma CITAD, wanda aka shirya a shafin Internet, akan cin zarafin da ake yiwa mata a manyan makarantun gaba da sakandire a jihar Kano.

Taron ƙarawa juna sanin wanda ya ɗauki tsahon awanni 3, an yi muhawara akan samar da ilimi da kuma cin zarafi ta hanyar lalata, cin zarafin mata ta hanyar lalata a manyan makarantun da ke jihar Kano.

Kabiru Dakata wanda ya nuna matuƙar takaicinsa a game da yadda ake ƙara samun cin zarafin mata ta hanyar lalata a manyan makarantun da su ke jihar Kano, ya ƙara da cewa wani bincike da su ka gudanar a jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da kuma Kwalejin ilimi da su ke jihar Kano, ya bayyana cewa fiye da kaso 51 na ɗalibai mata suna fuskantar zagi, da cin zarafi ta hanyar lalata, a wasu lokutan ma Malamai da ma’aikatan makarantun na yi musu fyaɗe ta hanyar yi musu barazana akan harkokin karatunsu.

”Sakamakon binciken ya nuna cewa kaso 45 na ɗalibai mata sun fuskanci runguma ko kuma sumbatarsu (Kiss) daga Malamansu, yayin da kaso 36 su ka fuskanci kalaman batsa tare da neman buƙatar yin lalata da su daga Malaman na su, sai kuma kaso 10 da Malaman su ka yi lalata da su, ragowar kaso 6 kuma aka yi musu fyaɗe”

Hakazalika babban daraktan na CAJA ya bayyana irin yanayin da ɗalibai mata su kan tsinci kan su a lokacin da su ka buƙaci wani taimako daga Malaman na su, wanda su kuma su kan yi amfani da wannan damar wajen cimma buƙatarsu.

Kabiru Sa’idu Dakata, ya ce rashin wata takaimaimiyar hanya da ɗaliban da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata za su kai rahoto, da kuma ƙarancin jami’an tsaron da za su baiwa ɗaliban kariya tare kuma da rashin dokokin da za su hukunta masu wannan mummunar ɗabi’ar, su ne manyan dalilan da ya sa ake yawan samun ƙaruwar lamarin.

”Za a cigaba da samun cin zarafin mata ta hanyar lalata tare da yi musu fyaɗe a manyan makarantu musamman a nan Kano, inda mu ka gudanar da binciken mu. Kuma zamu cigaba da gudanar da binciken, domin babu hanyoyin da daliban za su kai rahoton abin da ya ke faruwa da su.

”A mafi yawan lokuta idan aka samu faruwar irin wannan al’amarin za ka ji makarantun da abin ya faru a ciki sun kafa kwamitoci, wanda kuma a ƙarshe wannan kwamitin ya kan ɗauki watanni kafin ya fitar da sakamakon binciken, ko kuma a ƙarshe a cimma wata matsaya a sirrance ko a ja a rufe batun gaba daya”

”Mun lura cewa akwai ƙarancin jami’an tsaron da su ke manyan makarantun gaba da sakandire da za su lura da ɗalibai mata. Haka kuma dokokin mu ba su da ƙarfin da za su hukunta masu irin wannan mummunar dabi’ar da hakan zai sanya su zama abin misali”

A ƙarshe jami’in yaɗa labarai na Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani da ci gaban al`umma CITAD, Ali Sabo, ya ce cibiyarsu tana kokarin ganin ta wayar da kan mutane akan samar da dokokin da za su rage cin zarafin dalibai mata ta hanyar lalata a jihar Kano.