Karanta yadda ake ‘cin zarafin matan Nigeria a Facebook’

Shugaban Facebook, Marck Zukerberg ya ziyarci fadar shugaban da ya ziyarci Najeriya kwanakin bayaHakkin mallakar hotoSUNDAY AGHAEZE
Image captionShugaban Facebook, Marck Zukerberg ya ziyarci fadar shugaban da ya ziyarci Najeriya kwanakin baya

Wani bincike ya nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma’abota shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook.

Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau’i na tauye ‘yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da shi.

Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al’umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.

Social media
Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau’i na tauye ‘yancin mata

Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Muhammad Awwal Garba daga hukumar Hisbah ta jihar Kano da Maryam Ado Haruna, jami’a a wannan cibiya ta fasahar sadarwa da aka fi sani da CITAD, inda suka yi masa bayanin yadda girman matsalar take.