Kashi 40 Ne Na Ƴan Najeriya Ke Amfani Da Intanet – CITAD

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, ta koka akan yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta gaza haɗa wani adadi mai yawa na al’ummar ƙasar nan da fasahar intanet, wanda hakan zai ba su damar da za a dinga damawa da su a harkokin al’amuran ƙasar nan da ma abin da ya shafi duniya.

Haka kuma CITAD ta ce samar da fasahar intanet ɗin ga ɗimbin al’ummar musamman mazauna yankunan karkara zai taimaka ƙwarai da gaske wajen magance matsalolin da al’ummomin ke fuskanta tare da ba su dama wajen amfana da cigaban zamani a harkar fasahar sadarwa.

Jawabin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar bayan taron yini ɗaya na masu ruwa da tsaki na kungiyoyin fararen hula wanda cibiyar ta CITAD ta shirya.

Taron wanda ya gudana a fasahar sadarwa ta Zoom ya mayar da hankali kan yadda za a fahimtar tare da faɗakar da jama’ar ƙasar nan yadda za a samarwa da al’ummar yankunan karkara fasahar zamani domin su amfana da sauyin zamani, wanda hakan ɗaya ne daga cikin manyan ayyukan da cibiyar ta CITAD ta himmatu ƙarƙashin ƙungiyar Association for Progressive Communications (APC), tare da tallafin ofishin ƙasar Birtaniya mai lura da cigaban ƙasashe rainon ƙasar wato United Kingdom’s Foreign, Commonwealth and Development Office (FCDO), ta cikin shirinsu na Digital Access Programme (DAP).

Hakazalika sanarwar bayan taron ta ce adadin mutanen da su ke shafukan intanet sun kai 298,823,195, yayin da mutane 297,536,702 ne kawai su ke amfani da intanet a harkokin su na yau da kullum, wanda hakan ke nuna cewa kaso 40 ne kacal na Æ´an Najeriya ke amfani da intanet.

Sanarwar ta ƙara da cewa mafi yawan al’ummar da su ke zaune a yankunan karkara ba su da damar samun fasahar intanet ɗin sakamakon yadda manyan kamfanunnukan sadarwa ke ƙauracewa sanya turakunansu a yankunan saboda tsammanin rashin samun riba.

A ƙarshe cibiyar ta CITAD ta yi kira da gwamnatin tarayya da sauran ƙungiyoyin fararen hula da su haɗa hannu waje guda domin samar da dokokin da za su tilasta samarwa da yankunan karkara hanyoyin sadarwa domin su ma a dinga damawa da su a ɓangaren cigaban zamani musamman abubuwan da su ka shafi cigaba da magance dukkanin wani ƙalubale.