Want create site? Find Free WordPress Themes and plugins.

Wani rahoto daga kungiyar taimakon kai da kai mai suna Center for Information Technology and Development (CITAD) ta ce a tarihin majalisar dattijan Najeriya, mata 36 kadai suka taba samun zama sanatoci tun 1999, kamar yadda jaridar The Nation online ta ruwaito. Rahoton CITAD din ya bayyana ne a wani taron horar da manema labarai da ta shirya a birnin Yola da ke jihar Adamawa. Kungiyar ta ce tun daga 1999 majalisar tarayyar ta samu mambobi 654 ne kuma gurbi 618 maza suka cike shi inda matan suka ciki 36.
Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu – Bincike Source: Facebook An samu sanatocin 654 ne ta hanyar zabe tun bayan fara mulkin damokaradiyya a Najeriya. A kowanne lokacin zabe kuwa ana samun sanatoci 109 da ke wakiltar yankuna daban-daban na kasar nan. Rahoton ya bayyana cewa, a cikin sanatoci 109 na 1999 an samu mata uku ne kacal. A 2003 an samu hudu, a 2007 an samu takwas, a 2011 an samu bakwai, a 2015 an samu 8 sai kuma 2019 an samu shida. KU KARANTA: Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya A wani bincike mai zurfi kuwa, an gano cewa zai yuwu yawan sanatocin su gaza kai 36 saboda wasu matan ba sau daya suka lashe zabe ba. Misali ita ce Chief Remi Tinubu wacce ta ci zabe sau uku. Hakazalika a bangaren mazan za a iya samun kasa da 618 don akwai sanatocin da ba karonsu na farko kenan a majalisar dattijan ba. Rahoton CITAD din ya bayyana rashin shigar mata siyasa da kuma tsangwama da kalaman kiyayya da mata masu burin siyasa suke fuskanta. Rahoton ya bayyana cewa, akwai kalaman kiyayya da kuma na nuna banbancin jinsi wanda ake wa mata masu burin siyasa. A kan kwantanta su da karuwai da sauransu. Hakan kuwa na taka rawar gani wajen cire burin siyasa daga zukatan mata kuma yana hana su cin zaben. CITAD wanda ke da babban ofishi a jihar Kano ya horar da ‘yan jaridu ne tare da hadin guiwa NDI da kuma jami’in hukumar, Hamza Ibrahim.

Did you find apk for android? You can find new Free Android Games and apps.

Leave a Reply

Your email address will not be published.