“Mata Ne a Baya a Fannin Kimiyya Da Fasaha”

A ranar 11 ga watan Fabrairun kowacce shekara ne ake bikin ranar wayar da kai game da gudunmawar mata ga harkar kimiyya da fasaha a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ita da hukumominta sun lura cewa a shekara 25 da ta wuce, an samu wawakeken gibi a tsakanin mata da maza a harkar kimiyya da fasaha a duniya.

Babban abin takaicin ma, a cewar Majalisar, shi ne matan, koma-baya suka kara samu a harkar, a maimakon ci gaba.

To a kan haka BBC, ta tattauna da wata jami’a a cibiyar fasahar sadarwa da bunkasa al’umma wato CITAD, Maryam Ado Haruna, wadda ta ce gaskiya an bar mata a baya a wannan bangare, kuma hakan baya rasa nasaba da wasu dalilai da suka hada da al’ada, musamman a arewacin Najeriya, inda ake ganin ire-iren wannan karatu na kimiyya da fasaha na ‘ya’ya maza ne kawai.

Maryam Ado, ta ce dalili na biyu kuwa shi ne koma bayan da mata suka samu a harkar ilimi, tun da sau da dama a wasu wurare ba a bari mata suyi zurfin ilimi ake aurar da su.

Dalili na uku kuwa inji jami’ar shi ne, rashin wadanda ‘ya’ya matan za su gani suyi koyi da su a wannan fanni.

Yadda Tunkiya ta rikita masana kimiyya

Addinin Musulunci bai hana binciken kimiyya ba — Hayat Al-Sindi

Maryam Ado, ta ce bisa la’akari da wannan koma baya da mata suka samu a bangaren kimiyya da fasaha, cibiyarsu na kokari wajen wayar da kan mata da kuma iyaye a kan su rinka barin ‘ya’yansu mata na shiga a dama dasu a bangaren kimiyya da fasaha.

Jami’ar ta ce, yakamata a rinka wayar da kan mutane game da rawar da mata za su taka a fannin kimiyya da fasaha, domin hakan zai matukar taimakawa a samu ci gaba a kowacce al’umma.