Paradigm Initiative da CITAD sun gudanar da taro akan muhimmancin kare bayanan sirri

A ƙoƙarin su na ganin ƴan Najeriya sun fahimci amfani tare da muhimmancin kariya ga bayanan sirri wato Data Protection, a yau Talata ƙungiyar Paradigm Intiattive Nigeria (PIN) da haɗin gwiwar Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, sun gudanar da wani taro na musamman ga ƙungiyoyin cigaban al’umma da ɗalibai akan muhimmancin lamarin.

 

Taron wanda a gudana a Otal din Bristol Palace da ke Kano, ya mayar da hankali akan wayar da al’umma akan alfanun kare bayanan sirri na mutane.

 

Jami’a a ƙungiyar a ƙungiyar ta Paradigm Intiattive Nigeria (PIN), Khadija Usman ta ce sun shirya taron ne dan ƙara wayar da kan jama’a akan dokar kare bayanai wanda hakan zai taimakawa ƴan Najeriya wajen kare musu bayanan su na sirri.

 

 

 

Khadija Usman ta ƙara da cewa akwai buƙatar kare dukkanin wani bayani da za a iya binciko mutum da shi, wanda ya haɗa da bayanin bankin da mutum ya ke amfani da shi.

 

Ali Sabo, wanda jami’i ne a cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, ya bayyana cewa babban dalilin shirya taron shi ne a ƙara wayar da kan ƴan Najeriya akan muhimmancin kare bayanan sirri, wanda hakan zai taimaka wajen ganin ta yi gwamanati azama kan rattaba hannu akan dokar kare bayanai.

 

Mahalarta taron dai sun bayyana jin daÉ—insu a game da wannan taro da kungiyar Paradigm Intiattive Nigeria (PIN) da haÉ—in gwiwar Cibiyar CITAD su ka shirya.

 

Haka kuma taron ya samu halarcin kungiyoyin fararen hula da na É—alibai da kuma É—aiÉ—aikun mutane.