Tattauawa Ta Musamman Da Ado Sanusi Sabon Gida Akan Wayar Da Kan Masu Bukata Ta Musamman Akan Allurar Rigakafin Korona

A ranar Alhamis 29 ga watan Aprilun shekarar 2021, cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban a’lumma CITAD, ta gudanar da wata tattaunawa ta musamman akan yadda za a wayar da kan masu bukata ta musamman akan allurar rigakafin Korona.

 

A lokacin tattaunawar Malam Ado Sanusi Sabon Gida ya bayyana irin yadda cutar annobar Koronar ta shafi masu buƙata ta musamman a ɓangaren tattalin arziki da kuma walwala.

 

Idan ya bayyana cewa da yawan masu buƙata ta musamman sun rasa ayyukansu sakamakon sanya dokar kulle, wanda hakan ya mayar da su mabarata.

 

Haka kuma Ado Sanusi Sabon Gida ya zargi hukumar daÆ™ile yaÉ—uwar cututtuka ta Æ™asa NCDC akan yadda ta yi biris da masu buÆ™ata ta musamman a lokacin da ta ke aikin gangamin wayar da kan al’umma a game da cutar Korona.

 

Haka zalika, Ado Sanusi Sabon Gida ya ce tuntuni masu buƙata ta musamman na bin dokokin da Hukumomin lafiya su ka gindaya domin kariya daga cutar ta Korona. Ya lissafa cewa su kan yi amfani da Takunkumin rufe baki da hanci da kuma wanke hannu da ruwa mai sinadarin sanitaiza da bayar da kuma tazara.

 

Ya Æ™ara da cewa za su cigaba da wayar da kan masu buÆ™ata ta musamman akan amfanin karÉ“ar allurar riga-kafin cutar ta Korona, La’akari da irin alfanun da riga-kafin ke da shi da kuma hatsarin da cutar ke tattare da shi.