Alakar Kalaman Batanci A Nijeriya

Isah Garba
Babban Jami’in Shirye Shirye na Cibiyar Fasahar Sadarwa da cigaban Al’umma.

Kamar yadda muka yi bayani akan abubuwan da ke sanya mutane suyi kalaman batanci a makon da ya gabata, ya kamata wannan makon mu duba yadda akalar kalanman batancin dake ruruwa a Nijeriya, ta karkata don sake gane abubuwan da masu kalaman batancin kan fake dasu wajen yada kalanman, da kuma samun damar kama zukatan mutane ta hanyar su.

Kamar yadda muka yi bayani a baya a kwai alkaluman kalanman batanci a Nijeriya wacce cibiyar CITAD  ke bibiya a shafukan sada zumunta na yanar gizo da taimakon cibiyar MacAurthur Foundation. Wadannan alkaluma sukan nuna mutanen da ke yin kalaman batancin, a shafukan da suke amfani dasu wajen yada kalaman nasu, bangaren da suke kalaman akai, misali, siyasa da addini da fadan makiyaya da manoma da rigimar yan aware na Biyafara da kabilanci da kokarin jan wasu su shiga kungiyoyin ta’adanci da sauransu. A irin wadannan bangarori tun bayan zaben gamagari na shekarar 2015 lokacin da kalaman batancin lokacin da kalaman ba zabe batancin suka yi ta hauhawa a kan al’amuran da suka shafi siyasa da yakin neman zabe. Bayan zaben kanda sai suka lafa amma,  an a gama wannan sai kalaman suka chanja yanayi da akala ta yadda suka koma hauhawa cikin gaggawa kuma a kan abubuwan da suka fi komai tasiri a rayuwar da Nijeriya, wato bangaren kabilanci da addini. Juyawar kalaman batanci ga wadannan bangarori guda biyu masu mahimmanci a rayuwar yan kasar nan babbar barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban wannan kasa da al’ummarta, kuma matukar ba an samar da hanyoyin datsewa da magance wadannan matsaloli ba Nijeriaya na fuskantar mummunar barazana da ka iya jefa kasar cikin mummunan yanayi. A cikin wadancan alkaluman, sun nuna cewa a cikin shekara biyun da suka gabata 2015 da 2016 an samu sun nuna cewa mafiya yawan kalaman batancin sama da kashi tamanin bisa dari sun karkata ne zuwa ga wadancan bagarori. Haka kuma idan ka duba misali a cikin kalaman batancin da a kan yi a kan addini sukan faru tsakanin addinai mabambamta da kuma tsakanin addinai daya amma da bambamcin akida.

A kan samu irin waddancan kalamai tsakanin akidu mabambamta. A cikin addinin kirista kamar yadda a ke samu tsakankin Dariku da Izala ko Salafiyya ko  kuma a tsakanin Salafiyya da Izala a gefi guda da Shia a daya bangaren. Daga cikin abubuwan da shi wancan nazari da bincike na CITAD ya gano sun hada da yadda bangarori kan aibanta ko su ci zarafin  mutuncin Malamai da sauran ababen girmamawar wani bangare da suka saba dashi. A akida ko addini. Lalacewa da barnar dake cikin irin wadannan kalaman batanci a wadannan bangarori ya kai ga yadda za ka ga Kirista yana kalaman batanci a kan Musulmi amma sai kaga yana taba Allah da kansa ko kuma ka ga Musulmi yana son kalaman batancin a kan Kirista sai ya zarce yana taba Yesu (Jesus Christ) Annabi Isah. Haka kuma abin yake a abin da ya shafi kabilu yadda zaka ga cewa ‘yan wata kabila suna kalaman batanci a kan wata kabila ba kawai ta muggan kalamai a kan ‘yan kabilar kawai ba, amma a mafiya yawan lokuta ta hanyar wulakanta ababen girmamawar wannan kabila ko siffata su da munanan siffofi. Haka kuma irin wadannan halaye kai kace ma kara hauhawa suke  a cikin al’umma musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo. Kuma matukar muka barshi ya ci gaba ranar da daya bisa goma na irin wadannan kalamai ya fara yawo a cikin mu’amalarmu ta zahiri tashin hakali da hatsaniyar da zata faru sai dai Allah Ya kiyaye.

Maye yake kawo irin wadannan kalaman? Duk mai biyiyar irin wadannan kalamai zai shiga damuwa kwarai da gaske  da kuma tunanin me yasa mutane ke irin wadannan kalamai? Bincike ya nuna cewar a kwai wasu abubuwa da suke kawo irin wadannan kalamai, kuma ba za’a taba magance kalaman ba face an magance abubuwan da ke kawo su. Wadannan abubuwa sun hada da: Rashin cikakkiyar fahimtar bambamce-bambancen da ke tsakanin mu ko dai ta bangaren addini ko kabila. Munanan karantarwar addini da yake cusawa mabiya gaba da rashin girmama fahimta da addinan wadansu mutane.

Mummunar siyasar kabilancin da aka jefa a tsakanin ‘yan Nijeriya da yadda ya zama an an raba yaga su tsaninsu ta hanyar kabilanci da bambamcin addini. Karancin sanin tasiri, da yalwar da shafukan sada zumunta na yana gizo suke dashi ta yadda mafiya yawa da cikin masu amfanin da wadannan shafukan sukan ji kamar cewa suna magana kawai da abokan huldar su a kan shafukan ba tare da sanin cewa duk lokacin da wani yayi wani rubutu a yanar gizo ya tura wannan rubutun, to rubutun ya zama ba nasaba, ya zama na dukkan ma’abota amfani da shafunkan, a wanna ni lokaci ma har da masu zuwa daga baya. Wannan rashin sanin shi yasa zaka ga mutum ya na rubuta wani abu a kan wasu al’umma mutane da kabila ko addini wanda idan da sun san cewa wadannan mutanen zasu iya sanin abinda suka rubuta da zasu ji kunya, amma wannan rashin sanin sai yarda su iya rubuta abubuwan da suke rubutawa.

TA YAYA KUMA WAYE ZAI MAGANCE WADANNAN NNAN MATSALOLIN?

Idan ana son a magance wandanan  matsaloli  dole ne duk wani  mai ruwa da tsaki su ya bada gudunmawarsu  wajen yin haka. Saboda haka:

  1.   Dole ne malaman addini su kiyaye irin furucin su wajen wa’azi da sauran fadakarwar addini, su kiyaye ingiza mabiya wajen kyamar mutanen al’ummar  da suka saba dasu a fahimta ko addini ko kabila.
  2. Haka kuma duk wani wanda ke mu’amala da yanar gizo, musamman shafukan sada zumunta ya gane cewa dukkan abun da yasan idan ya fade shi a gaban wasu mutane zai ji kunya, ko zai bata musu rai, ko zai tunzura su, ko zai bata dangantar da ke tsaninsa da su, ko da kabilar sa to ka da ya rubuta shi a shafukan sada zumunta, domin kuwa da zarar ya rubuta to ya sani mutanen da baya son su gani zasu iya gani kuma idan yana jin cewa yana da abokan hulda dubu biyar ne, idan ya rubuta abu akan samu mutum dubu daya daga cikin su su kai abin da ake ce masa ‘sharing’ kuma kowanne daga cikin su yana da abokan hulda dubu biyar ka ga ka rubuta abu don mutane dubu biyar amma yanzu mutane dubu biyar sau dubu dari biyar ne zasu karanta.
  3. Haka kuma dole mu gane cewa dukkan abun da bama son wani ya fada a kan mu dole muma mu kiyaye fada wa wasu irin sa kuma matukar muna da wadanda muke girmama wa ko addinin da muke bi to mu kiyaye wulakanta addinin wadansu idan bama son a wulakanta wadanda muke girmama wa to mu kiyaye wulakanta na wasu.

    Idan muka bi irin wadannan hanyoyi  muka kuma kiyaye abubuwan da muke rubutawa tare da daukan matakan wayar da kan al’umma a kan hatsarin kalaman batanci da kuma hatsarin rubuta dukkan abun da muka ga dama a shafukan sada zumunta na yanar gizo, zai rage yawan kalaman batancin dake hauhawa a shafukan yanar gizo a lokaci guda kuma ya rage hatsarin da ke fuskantar wannan kasa na fadawa cikin rigingimu sakamakon  yawan wadannan kalamai da suke neman lalata mana zamantakewa da kuma bata watsa mana tattalin arzikin kasa  sakamkon rashi zaman lafiya.