CITAD Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Al’umma Kan Amfanin Fasahar Sadarwa Ga Mazauna Yankunan Karkara.

A Æ™oÆ™arin ta na ganin an samarwa da al’ummar da su ke zaune a yankunan karkara, cibiyar bunÆ™asa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, ta gudanar da wani taro na wuni É—aya wanda ya gudana a cibiyar fasahar sadarwa ta Æ™auyen Pasepa a yankin Æ™aramar hukumar Bwari da ke Abuja, ya mayar da hankali ne akan wayar da kan jama’ar Æ™auyen kan amfanin samar da fasahar sadarwa.

Tun da farko cibiyar ta CITAD ce ta ke gudanar da wani aiki mai taken community network project wanda ya ke ƙarƙashin kulawar Association for Progressive Communications (APC) da kuma United Kingdom’s Foreign, Commonwealth and Development Office (FCDO), ta cikin shirin su na Digital Access Programme (DAP).

A lokacin gudanar da taron jami’a mai kula da shafukan sadarwar zamani ta cibiyar CITAD É—in, Harira Abdurrahman Wakili, ta gabatar da jawabi akan muhimmanci tare da alfanun da ke tattare da samar da fasahar sadarwa ga mazauna yankunan karkara.

Harira Wakili ta ce a halin da ake ciki a yanzu harkokin kasuwanci da ilimi da sauran abubuwan da su ka shafi rayuwar al’umma sun koma dandalin intane, wanda kuma akwai buÆ™atar a samarwa da mazaunan yankunan na karkara fasahar zamanin domin su ma a dama da su.

Suhail Sani Abdullahi wanda shi ma jami’i ne a sashen fasaha na cibiyar ta CITAD, cewa ya yi samarwa da al’ummar da su ke zaune a Æ™auyuka fasahar sadarwa zai taimaka Æ™warai da gaske musamman a É“angaren ilimi da kuma tsaro.

Ya ce idan ana batun fasahar sadarwa bai kamata a ce an ware wani bangaren al’umma ba domin hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta samar da fasahar sadarwar a dukkanin Æ™auyuka, musamman idan aka yi la’akari da cewa al’ummar da ke zaune a irin waÉ—annan yankunan su ke da mafi yawan kaso na al’ummar Najeriya.

Taron dai ya samu halarcin jama’ar wannan Æ™auye da kuma shugabbanin addini da na al’umma da kuma shugabannin kungiyoyin mata.

A ƙarshe cibiyar ta CITAD ta yi kira ga gwamnati da sauran ƙungiyoyin fararen hula da su zage himma wajen ganin an haɗa hannu guri guda ganin gwamnati ta samar da wata doka da za ta tilastawa kamfanonin sadarwa masu zaman kan su kafa turakunansu a yankunan karkara.