Amfani da shafukan sadarwa na zamani domin wayar da kan jama’a akan Allurar Riga-kafin Korona

A cigaba da wayar da kan al’umma akan amfanin da allurar riga-kafin Korona ke da shi ga lafiyar al’umma, Cibiyar BunÆ™asa Fasahar Sadarwa Da Cigaban Al’umma CITAD, ta kuma shirya wata tattaunawa ta musamman da wani masani akan shafukan sadarwa na zamani, Aliyu Samba akan yadda za a yi amfani da shafukan wajen faÉ—akar da al’umma irin alfanun da ke tattare da riga-kafin.
A cikin tattaunawar an yi wa @Aliyu_samba tambaya akan cewa  “akwai milyoyin al’umma da su ke amfani da shafukan sadarwa na zamani, ko yin amfani da shafukan wajen wayar da kan al’umma akan amfanin allurar rigakafin korona zai taimaka? @CitadHausa @kamalkano @CitadRadio @sagiru_ado
Inda Aliyu @Aliyu_samba ya bayar da amsa kamar haka “Kwarai kuwa zai taimaka matuÆ™a da gaske. Domin a yanzu idan muka ce da yawan mutane sun karkata ga shafukan sadarwa wajen neman ilimi da kuma wayewa akan al’amuran yau da kullum, to tabbas bamu yi karya ba. Kusan ma wannan shine mataki mafi tasiri a matakan isar da sako ga mutane”
Haka kuma ya bayyana Æ™alubalen da za a iya fuskanta wajen karÉ“ar allurar riga-kafin Korona É—in daga al’umma ba.
“Kalubale bai wuce dayan biyu ba, ”Rejection” ma’ana Æ™in yarda. Da kuma ”Misconception” ma’ana rashin fahimta a takaice. Za a maka fassara a ce ai kudi ka karba, kuma za a ki karbar gaskiyar da kake fada”
Ya ce amma akwai hanyar da ake bi wajen magance wannan suna da yawa, amma daga ciki. Hanyoyin su ne kamar haka:
“Akwai kokarin gina yarda tsakanin ka da al’ummar da kake isar wa da sako. Sannan kuma bude musu al’amuran da suka shige musu duhu takan amsa tambayoyin da suke sa su a shakka da hujjojin da zasu gansar dasu”
“Hakan zai yi tasiri sosai idan ya zama saÆ™on yana fitowa ne daga tushen da ya gina yarda tsakanin sa da al’umma. Sannan a yayin isar da sakon akwai buÆ™atar abinda masana ke cewa (SBCC). Social Behavioral Change Communication. Wani salon isar da sako ne da yake tasiri”
Haka kuma @Aliyu_samba ya ce akwai shafukan da su ke ƙoƙarin bayar da bayan akan amfanin allurar riga-kafin a cikin manyan harsunan Najeriya guda uku.
“Akwai shafuka da suke wannan kokarin matuka da gaske, wasu na kungiyoyi ne masu zaman kansu, wanda a misali zamu iya cewa ”CITAD”, Sannan akwai shafukan da ke mallakin wasu mutane ne masu tasiri da ake kira ”Influencers”, wanda zan riga shafi na a ciki”
A Æ™arshe @Aliyu_Samba ya ce gwamnati ce ke da alhakin sauya tunanin al’umma akan yadda za su aminta da karÉ“ar allurar riga-kafin Korona.
“Wajen sauya tunanin mutane game da wani al’amari. Gwamnati ita ce za ta yi wannan dan samar da daidaito da aminci tsakanin ta da wadanda take mulka akan sha’ani irin wannan mai hatsari. Sai an haska hatsarin tarwai an ganshi ta sigogi da yawa sannan aminci zai samu’