CITAD ta tattauna da bangarorin jama’a dan ganin yadda za’a dama da mata da matasa a siyasa.

Sakamakon giɓin da ke tsakanin mata da kuma matasa a harkokin siyasa da kuma shugabanci a fadin ƙasar nan, CITAD da haɗin gwuiwa da Actionaid ta tattauna da bangarorin jama’a dabam-dabam dan ganin yadda za’a dama da matasa da mata a harkokin siyasa da kuma shugabanci.

John Otara wanda yake Jami’in Kula da Shirye-shirye da sa ido na CITAD, ahine wanda ya farayiwa mahalarta taron jawabi kan abinda shirin/tattaunawa ta kunsa, inda ya fara da bayanin dalilin CITAD na fara gabatar da wannan shirin tare da hadin gwuiwar Actionaid, sakamakon gabatowar babban zaben shekararar 2023. Haka zalika dai ya bayyana kananan hukumomin da wannan shirin zai shafa, da kuma wanda ke da ruwa da tsaki a cikin shirin.

Da yake nasa jawabin Isa Garba Wanda yake babban jami’in shirye-shirye na CIbiyar yace wannan shirin an fara shi ne dan ganin yadda rukunin al’umma daban-daban zasu bada gudunmawa wajen ganin an tafi da mata da matasa a harkokin siyasa da shugabanci.

Ƙananan hukumomi 8 cibiyar ta zaba a ciki da wajen birnin kano la’akari da tasirinsu, da kuma tasirin jihar kano (mai yawan jama’a a ƙasar) da kuma irin tasirin da zaau kawo.

Daga cikin mahalarta taron akwai ƴan jam’iyyun Siyaasa daga PDP da PRP da kuma Masu gabatar da shirye-shiryen siyaa a gidajen radion Arewa, Freedom da ƴan kungiyoyin sa kai daga kananan hukumomi daban-daban.

Nura Ma’aji wanda yake shugaban Matasan Jam’iyyar PDP (kwankwasiyya) ya nuna jin dadinsa da kuma bayyana wasu daga cikin dalilan dake sa koma bayan matasa da mata a siyasance.

Shi kwa a nasa bangaren tsohon Shugaban Matasan Jam’iyyar PRP ya bayyana irin yadda matasa ke girmama neman kudi dana goro maimakon maida hankali wajen ganin yadda zaau bawa al’umma gudunmawa.

Cikin wadanda shirin yake sa ran tuntuba da bada gudunmawa a shirin sun Hada da Tsoffin ƴan Siyasa, Ƴan wasan Kwaikwayon Kannywood, Mallamn Addini, Masu rike da sarautun gargajiya, gidajen radio da sauransu.