Matsalar Ruwan Sha A Ƙaramar Hukumar Ƙunchi

 

Matsalar Ruwan Sha A Ƙaramar Hukumar Ƙunchi A Jihar Kano
Ruwa aka ce shi ne ginshikin rayuwa, don haka samar da tsabtatatcen ruwan sha ga jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowacce gwamnati.
Sai dai abin ba haka ya ke a Æ™aramar hukumar Ƙunci da ke jihar Kano, domin al’umma a mazabun Shuwaki da Gwarmai na fama da mummunar matsalar ruwan sha, inda su kan yi tafiya mai nisan gaske kafin su kai ga samun ruwan sha.
Tawagar Cibiyar BunÆ™asa Fasahar da Cigaban Al’umma CITAD sun kai ziyarar gani da ido zuwa waÉ—annan yankunan da su ke fama da matsanancin wadataccen ruwan sha, inda mazauna garuruwan su ka bayyana irin wahalar da su ke sha kafin su samu ruwan da za su yi amfani da shi a gidajensu.
Al’ummar Æ™auyukan Baji da Limamai da Agalawa da Kuku da Gwadama da Kargo da kuma Hayin Malamai na zuwa wata rijiya wacce wani mutum mazaunin jihar Kaduna ya gina a yankin Kwardakwalle inda su ke É—ebo ruwan da za su yi amfani da shi.
Dagacin Baji Malam Umaru Salisu wanda ya samu wakilcin Muhammadu Umaru ya bayyana cewa suna fuskantar matsalar ruwan sha a yanku nan na su, domin su kan yi tafiyar a kalla kimanin kilomita Biyar (5) zuwa Bakwai (7) kafin su kai ga inda za su samu ruwan da za su yi amfani da shi.
A nasa É“angaren mai unguwar Gwalaida Malam Haruna Mai Unguwa Dan Gidan Zubairu, ya bayyana irin yadda matsalar rashin ruwan ke hana Æ´aÆ´ansu zuwa makaranta.
Mai Unguwa Haruna ya ce ƙauyukan da su ke zagaye da Gwalaida kan taso ƙafa da kafa su zo Kwardakwalle neman ruwan sha, duk da irin nisan da ke tsakaninsu da rijiyar.
Yahuza Muhammad Yahuza Kuku yana ɗaya daga cikin magidanta da mu ka same shi a bakin rijiyar yana jiran layi ya zo kan sa ya debi ruwan, ya bayyana cewa haƙiƙa suna tsananin fama da matsanancin rashin ruwan sha a ƙauyukan na su domin a wasu lokutan har kwana su ke a wajen diban ruwan.
Ya ƙara da cewa sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin hukumomi a yankin ta hanyar kai musu kokensu amma har yanzu shiru babu labari
Wani matashi da mu ka zanta da shi mai suna Abdullahi Mustapha ya ce yadda su ke fama da matsalar ruwa a yanku nan na su kan tilasta musu ficewa zuwa cirani.
Matsalar ruwan sha da fannin ilmi da wutar lantarki na daga cikin abubuwan da mahukunta a Najeriya ke gangamin yakin neman zabe da su. Sai dai har yanzu babu É—aya da aka magance
A Æ™arshe al’ummar wannan yanki sun yi kira ga hukumomi da sauran kungiyoyi da su kai musu agajin gaggawa akan wannan matsala ta ruwan sha.