Rahoton ICT quiz na CITAD 18th November 2021 KUST Wudil

Harkar koyo da koyarwa na canja salo, sannu-sannu zuwa amfani da fasahar sadarwa dan koyarwa tare da koyo. Duba da irin yanayin samun damar koyarwar wa a saukake da kuma koyan a saukake. 

Tun shekarar 2001, cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta yunkuro da wani kaci-kaci kan fasahar sadarwa a tsakanin manyan makaratun sikadire da ke jihar kano dan ganin an zaburar da su amfani da kuma damarmaki da ke cikin karantar harkar sadarwa. 

Wannan shine karo na ashirin (wato shekara ashirin kenan) da aka gudanar da kaci-kacin a Jami’ar kimiya da fasaha da ke garin Wudil. 

Da yake jawabi yayin bude kaci-kacin, wakilin babban daraktan cibiyar Mallam Isyaku Garba ya fara ne da batu kan alfanun dake cikin kimiyar da fasaha da kuma dalilin da yasa cibiyar ta CITAD tag a dacewa da kuma yunkurin gudunar da wannan kaci-kaci a tsakanin makarantun sikandire. 

Ya kare da cewa “ cibiyar CITAD a shirye take wajen bayan da gudunmawa ta harkar koyar tare da habaka harkar fasahar sadawar a tsakanin al’umma” 

Kimanin makarantu 32 ne suka halarci kici-kacin bisa sahalewar ma’aikatar ilimi ta jihar kanno da kuma hukumomin da ke karkashenta. Daga cikin makaratun da suka fafata a yayin kaci-kacin akwai makarantar staff school Wudil, G.G.S.S Gwarzo, M. S. S Gaya, G.S.S Garko da sauransu. 

Dawakin Tofa Science ce tazo ta daya bayan zuwa zageyen karshe da maki goma 14, sai kuma Government commercial secondary school Kano tazo ta biyu da maki 12 sai kuma Government secondary school tudunwada tazo ta uku da maki . Bayan kamala kaci=kacin an raba kyauututtuka ga wadanda suka zamu zakaru, wanda suka hada da computer tafi da gidanka, printer da sauransu. 

Haka zalika ma cibiyar ta karrama wasu daga cikin hukumomi da cibiyoyi da kuma manyan makarantun gaba da sikandire da suka bada gudunmawa wajen tabbatuwar kici-kacin. 

Cibiyar CITAD ce de ke daukar nauyin shirin tare da hadin gwuiwar hukumomin gwamnati, yan kasuwa, mutane a dai-daiku, kamfanunka da sauransu.