Sai an yaƙi cin hanci da rashawa sannan za a samu nasarar magance ƙalubalen tsaro a Najeriya – CITAD

Babban daraktan Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD, Mallam Yunusa Ya’u ya bayyana cewa yaƙi da matsalar tsaro da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ke yi ba zai taɓa yin nasara ba muddin akwai cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatu da jami’an gwamanati.

Malam Yunusa Ya’u ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a lokacin da ya ke gabatar da wasu littafai da cibiyar ta wallafa. Littattafan da su ka haɗa da The Compromised State: How Corruption Sustains Insecurity in Nigeria” da kuma Context and Content in Hate Speech Discourse in Nigeria”.

Littattafan da aka rubuta su cikin harshen Ingilishi, inda littafi na farko ya mayar da hankali ne akan yadda cin hanci da rashawa ke ƙara rura wutar rikicin da ke faruwa a Najeriya, sai kuma dayan wanda ya mayar da hakali akan illar da kalaman batanci kan haifar a cikin al’umma tare da kawo tashin – tashina.

Babban daraktan ya ce kalaman ɓatanci da cin hanci da rashawa su na ƙara rura wutar rikici a Najeriya, kuma abu ne mai wahala a samu nasara akan yaƙin da ake da ayyukan ta’addanci muddin ba a yaki wadannan abubuwa ba to abu ne mai wahala a samu zaman lafiya da cigaba.

Malam Yunusa Ya’u ya ce a sakamakon cin hanci da rashawa a ɓangaren tsaron kasar nan ya sanya masu riƙe da ɓangaren ke burin ganin an cigaba da samun rashin kwanciyar hankali domin kawai su dawwama akan shugabancin.

Hakazalika, babban daraktan ya ce al’amarin yaƙi da cin hanci da rashawa bai kamata ya zama aikin gwamnatin tarayya kaɗai ba, ya kamata jihohi su kasance suna taka rawa wajen yaƙi da wannan mummunar ɗabi’ar.

Haka kuma ya buƙaci masu riƙe da mukaman gwamnati da kuma jagororin al’umma da su yi ƙoƙari su karanta wadannan littattafai domin hakan zai sanya musu karsashin yaki da cin hanci da rashawa.

A ƙarshe ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da kungiyoyin sa kai da su himmatu wajen zakulo abubuwan da za su wayar da kan al’umma akan haɗarin da tattare da cin da rashawa tun daga tushe.